Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Uganda: Jama'a na gudun hijra daga zabtarewar laka
Jami'ai a Uganda sun ce akalla mutum shida ne suka mutu sannan 17 suka jikkata sakamakon zabtarewar laka da ta faru da sanyin safiyar Laraba, a yankin Bududa da ke gabashin kasar.
Ana fargabar yiwuwar karuwar alkaluman wadanda suka mutu kasancewar har yanzu akwai mutanen da ba a gan su ba.
Ana yawan samun zabtarewar lakar a yankin da ke kusa da tsaunin Elgon wanda yake kusa iyakar kasar da Kenya.
Fiye da mutum 300 ne suka mutu a ibtila'in zabtarewar lakar a yankin a shekarar 2010.
Hukumomin a kasar sun yi hasashen cewa daruruuwan jama'ar yankin sun bar gidajensu inda suke neman mafaka a coci-coci da masallatai da kuma wurin 'yan uwa.
An kuma samu wani wawagegen rami sakamakon zabtarewar lakar a daya daga cikin kauyukan.
Yanzu haka masu aikin ceto na tantance irin asarar aka dubga.
Shugaban yankin, WIlson Watila, ya ce kauyukan ka iya fuskantar barazanar zabtarewar lakar idan dai har aka ci gaba da ruwan sama, al'amarin da zai jefa kauyuka da dama cikin hadari.
Gwamnati ta ce an bukaci fiye da mutum dubu 100 da su bar inda gidajensu da gaggawa.
A bara ma irin wannan ibtila'i ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 40, inda a watan Mayun wannan shekarar gwamnati ta fara aikin sake tsugunar da mutanen da ibtila'in ya daidaita.
To sai dai rashin isassun kudin gudanarwa da kuma taurin kan mutanen da ake son sake tsugunarwar sun zama tarnaki ga gwamnatin.