Za a tuhumi Ramaphosa kan rashawa

Wata sabuwar danbarwar rashawa ta rutsa da shugaba Cyril Ramaphosa na Afurka ta Kudu, kan zargin karbar kudaden tallafi gabannin yakin neman zabe.
Sai dai shugaban ya musanta wannan zargi, yayin da magoya bayansa suka ce bita da kullin siyasa ne kawai.
A shekarar da ta gabata ne Mista Ramaphosa ya shaidawa zauren majalisa cewa bai karbi ko taro a matsayin tallafi a lokacin yakin neman zabe daga wani kamfani na Afurka ta Kudu, da ya yi kaurin suna wajen janyo cece-kuce, a lokacin da yake gwagwarmayar jan ragamar jam'iyyar ANC mai mulki.
Amma daga bisani sai labarin ya sauya, inda aka gano Ramaphosa karya ya yi wa 'yan majalisar kuma ya bada hakuri ba tare da bata lokaci ba, sai dai ya fake da cewa shi ma an rufe shi baibai kan batun kudaden.
Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Afurka ta Kudu ta rawaito cewa da gangan Ramaphosa ya manta da 'yan majalisa tare da bukatar lallai a gudanar da bincike akan sa.
Sai dai wasu na ganin wannan sabuwar danbarwar rashawar akan shugaba Ramaphosa a matsayin gwagwarmayar karbe iko da jam'iyyar ANC da ita kan ta Afurka ta Kudu.
Tuni dai aka samu rarrabuwar kawuna a jam'iyyar tun zamanin tsohon shugaba Jacob Zuma, wanda aka tilastawa yin murabus a watan Fabrairun bara duk dai kan zargin rashawa.
Mataimakinsa Ramaphosa ne ya maye gurbinsa, tare da alkawarin magance matsalar cin hanci da rashawa da ta yi wa kasar dabaibayi da janyowa tattalin arziki koma baya.
A yanzu za a zuba ido a gani ko za a yi adalci da hukunta shugaban da ya yi ikirarin tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta kassara tattalin arzikin kasar sakamakon cin hanci da rashawa.










