Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mercy Johnson za ta fara sabon shirin talabijin kan girke-girke
Tauraruwar fina-finan kudancin Najeriya na Nollywood Mercy Johnson Okojie ta bayyana shirinta na fara gabatar da wani shirin talbijin mai suna Kitchen Talk show.
Ta shaida wa kafar Youthville a Legas cewa za ta rika gayyato fitattun 'yan fim a cikin shirin, inda za su rika tattaunawa game da rayuwarsu ta yau da kullum ana kuma yin girki a lokaci guda.
Har wa yau, shirin mai zango 13 zai karbi bakuncin taurari kamar Liz Benson da AY da Chigul da Omawumi da Niniola da Ufuoma McDermott.
Sauran sun hada da Lolo 1 da Maraji Busola da DakoloKemi 'Lala' Akindoju da Ill Bliss da Munachi, sai kuma 'yan uwanta wato Prince Odi da Purity da Henry da Angel Okojie.
Ta ce: "Mutane da dama suna tunanin cewa fitattun mutane na rayuwa cikin annashuwa dari bisa dari, amma abin ba haka yake ba.
"Na kira wannan shiri da suna "Kitchen Talk show" (wato Tattaunawa a dakin girki) ne saboda ina matukar sha'awar hira a kan abinci.
"Sannan kuma saboda muna yawan tattauna muhimman abubuwa da suka shafi rayuwarmu a dakin girki."
Ta kuma bayyana cewa an nadi shirin ne tun a shekarar 2018 a Pedini Bosch Kitchen, inda bakin shirin suka tattauna a kan zamantakewar aure da aiki da laifuka da kuma manyan abubuwan da suka shafi rayuwarsu.
Za a fara yada shirin daga 6 ga watan Yulin 2019 a tashar African Magic Showcase da karfe 5:00 na yamma agogon Najeriya duk ranar Asabar.