Mutum miliyan 70 sun bar muhallansu - MDD

An wallafa

Hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan mutanen da tashin hankali ya raba da muhallansu ya wuce miliyan 70, adadi mafi girma da aka taba gani a tarihi.

A kididdigar da hukumar ke fitarwa duk shekara, ya nuna mutanen da yaki ke tilastawa barin gida, na gagara samun wurin da za su zauna cikin kwanciyar hankali.

Kasar da ta fi samun sabbin masu neman mafaka a duniya a bara ita cce Venezuela.

Yayin da kasashe kamar Syria suke sahun gaba wajen yawan 'yan kasar da ke kwarara kasashe makwafta kamar Turkiyya da Lebanon don tserewa yakin basasar da suke ciki na kusan shekara takwas.

Kwamishinar hukumar 'yan gudun hijira ta MDD Filippo Grandi ya shaida wa BBC cewa matalautan kasashen da ke cikin tashin hankali na tsananin bukatar karin taimakon kasashe masu arziki don shawo kan matsalar.