Da gaske jarumin Kannywood Sani S.K. ya rasu?

Bayanan sautiDa gaske Sani SK ya rasu?
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren hira da Sani S.K.

Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood Sani Garba SK. ya musanta labarin da ke cewa Allah ya yi masa rasuwa.

A ranar Litinin ne wasu mutane da ke amfani da shafukan sada zumunta suka yi ta baza labaran karya a kan cewa ya rasu bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Da ma dai tauraron na fama da rashin lafiya.

A hirarsa da BBC, sani S.K ya ce yana nan da ransa kuma yana samun sauki.

Ya bayyana cewa har ya gaji da amsa wayar tarho domin irin yawan mutanen da suke kiransa domin su ji ta bakinsa a kan ko da gaske ya mutu.

Amma dai tauraron ya ce yana fama da ciwon suga kuma ya gano hakan ne cikin 'yan kwanakin nan da ya je asibiti.

A baya dai an yada labaran karya a kan mutuwar wasu fitattun taurarin Kannywood, ciki har da Sadiya Gyale da Sani Moda.

An rika yada labarin mutuwar jarumi Sani S.K a Facebook, kamar haka:

Kauce wa Facebook, 2

Babu karin bayanai

Ci gaba da duba FacebookBBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba.

Karshen labarin da aka sa a Facebook, 2