Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kamaru ta nada Seedorf a matsayin koci
Kamaru ta nada Clarence Seedorf a matsayin sabon kocin kungiyar kwallon kafa ta kasar bayan da yarjejeniyar da kasar ta so kullawa da tsohon kocin Ingila Sven-Goran Eriksson bata samu ba.
Tsohon dan wasan tsakiya na Real Madrid, da AC Milan da kuma Netherlands, Seedorf zai kama aiki tare da mai taimaka masa kuma abokin wasansa dan Holland Patrick Kluivert.
Daga baya cikin wannan watan za a sanar da tsawon yarjejeniyar da kwantaragin da ya sa hannu za ta kasance.
A baya Clarence Seedorf mai shekara 42 ya horas da AC Milan da Shenzen a China da kuma Deportivo La Coruna.
Amma bai wuce wata shida ba a dukkan wadannan wurare uku da yayi aiki.
Seedorf zai gaji Hugo Broos, kuma zai yi aiki na shekara daya tare da kungiyar kwallon kafa ta Kamarun kafin gasar kwallon kafa ta nahiyar Afirka ta 2019 ta fara.