Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Tafkin Victoria na fuskantar barazana
Masana kimiyya na gargadin cewa tafkin Victoria ,wanda shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrika , na fuskantar barazanar gurbacewa.
Tafkin Victoria shi ne tafkin ruwan dadi mafi girma a nahiyar Afrika, mai iyaka da kasashen Uganda da Kenya da Tanzania
Sun ce yawan kamun kifi da ya zarce kima tare da gurbatar muhalli ya kassara adadin kifayen da ake samu a cikinsa, abinda ke barazana ga rayuwar miliyoyin masuntan da suka dogara da tafkin.
Masanan sun ce gurbataccen ruwan dake kwarara cikin tafkin na haddasa dafi a cikinsa, yayinda takin da ke gangarowa daga gonaki ke kashe tsirran da ke rayuwa a cikin ruwan.
Kuwesi Edi na daya daga cikin masuntan da ke kamun kifi a tafkin kuma ya ce kifin da suke kamawa ya yi karancin kwarai.
Ya baya wuce kilo goma kuma a da su kan kama kifi kilo dari zuwa dari biyar.
Kuwesi ya ce yana matukar fargabar abinda zai faru nan gaba.