Mutane 24 sun mutu a turmutsitsi a India

Asalin hoton, EPA
An wallafa
Akalla mutane ashirin da hudu ne suka mutu a turmutsitsin da aka samu a wajen wani taron addini a arewacin Indiya.
Dubban mabiya addinin Hindu, karkashin koyarwar Jai Gurudev ne suka taru a Varanasi, a garin Uttar Pradesh, wanda gari ne mai tsarki a wurin mabiya addinin na Hindu da dama.
Ba a tabbatar da dalilin da ya haddasa turmutsitsin ba.
Sai dai, turmutsitsi ba sabon abu ba ne a Indiya, inda tarukan addini da na siyasa ke sa mutane ne cincirindo a wuri guda, kuma ba a iya tafiyar da tarukan yadda ya kamata.







