Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Super Eagles ta fara da kafar dama a wasan neman gurbin kofin Afirka
Super Eagles ta yi nasara a kan Saliyo da ci 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar kofin nahiyar Afirka da suka fafata ranar Alhamis.
Saliyo ce ta fara cin kwallo ta hannun Jonathan Morsay a minti na 11 da fara tamaula a filin wasa na MKO Abiola da ke Abuja, Najeriya.
Super Eagles ta farke ta hannun Alex Iwobi minti biyar tsakani, sannan saura minti biyar su je hutu ne Super Eagles ta kara na biyu ta hannun Victor Osimhen.
An buga karawar ba tare da 'yan kallo ba, sakamakon hukuncin Fifa, bayan yamutsin da ya faru a karawa da Ghana a Abuja, Najeriya.
Ghana ce ta ci Super Eagles da hakan ya hana Najeriya samun gurbin shiga gasar kofin duniya da za a yi a Qatar tsakanin Nuwamba zuwa Disambar 2022.
Najeriya za ta buga wasa na biyu a cikin rukunin farko ranar Litinin 13 ga watan Yuni, inda za ta ziyarci Mauritius.
Daya wasan rukunin farko da suka fafata ranar Alhamis, Guinea Bissau ta caskara Sao Tome And Principle da ci 5-1.
Ivory Coast ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2023.