Afcon 2021: Senegal ta ja ragamar rukuni na biyu a gasar kofin Afirka

An wallafa

Senegal ce ta daya a rukuni na biyu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da ake yi a Kamaru, duk da tashi 0-0 da Malawi ranar Talata.

Habib Diallo da Sadio Mane sun kusan ci wa Senegal kwallo, yayin da Malawi wadda aka bai fenariti daga baya aka soke, bayan da alkalin wasa ya tuntubi VAR, wato na'urar da take taimakawa alkalin wasa yanke hukunci.

Malawi ta sa ran buga fenaritin a minti na 74, sakamakon alkalin wasa da ya busa, bayan da Bouna Sarr ya ja rigar Gomezgani Chirwa.

Daga baya alkalin wasa Blaise Yuven Ngwa ya soke hukuncin, bayan da ta kalli abinda ya faru a VAR.

Malawi ta kare rukunin na biyu da maki hudu a mataki na uku, wadda za ta iya kai wa zagaye a daya daga hudun da za a zabo masu maki da yawa.

Senegal wadda ta yi ta biyu a gasar 2019 ta ci kwallo daya tal a bana kuma a bugun fenariri a wasan farko a cikin rukuni da Zimbabwe

Da wannan sakamakon Senegal za ta fafata da duk wadda ta yi ta uku a rukunin farko ko na uku ko kuma na hudu a karawar zagaye na biyu ranar 25 ga watan Janairu.