Pakistan ta kai hare-haren sama a Afghanistan
Ƙasar Pakistan ta ƙaddamar da hare-haren sama masu muni a kan iyakarta da Afghanistan, lamarin da ya kawo ƙarshen zaman lafiya na watanni da aka samu a yankin da ke fama da rikici.
Ministan yaɗa labaran Pakistan, Attaullah Tarar, ya bayyana a ranar Laraba cewa an lalata wurare hudu a wani hari da aka yi cikin tsari, wanda ya kashe ‘yan bindiga 26.
Amma gwamnatin Taliban a Afghanistan ta ce hare-haren sun kashe mutane 13, ciki har da yara 11.
Pakistan ta daɗe tana zargin Afghanistan da bai wa ‘yan ta’adda mafaka domin kai hare-hare a cikin ƙasarta, zargin da gwamnatin Taliban ke ci gaba da musantawa.
Wannan sabon rikici shi ne na farko tun watan Fabrairu, lokacin da ƙazamin faɗa a kan iyaka ya yi sanadin mutuwar ɗaruruwan mutane.
Ƙasashen biyu sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Oktoban bara bayan makonni na rikice-rikice masu muni.
Attaullah Tarar ya ce hare-haren sun zo ne a matsayin martani ga “sabbin hare-haren ta’addanci a Pakistan,” inda aka kai farmaki kan wuraren ɓuya da horar da ‘yan bindiga, da kuma wuraren ajiye makamai a yankin iyaka.
Tun bayan ƙazamin rikicin da ya faru a karshen watan Fabrairu, an samu arangama lokaci-lokaci, yayin da shugabannin duniya ke kira ga ƙasashen biyu da su dakatar da faɗa tare da rungumar zaman lafiya.