'Yan wasan Manchester United da za su bar kungiyar a bana

Man United out of Contract

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Juan mata yana daga cikin 'yan wasan Manchester United da kungiyar ta sanar za su bar Old Trafford a karshen kakar tamauala ta bana.

United ta sanar da jerin 'yan wasan da yarjejeniyarsu za ta ta kare da wadanda za su bar kungiyar a bana, bayan da ta dauko sabon koci, Erik ten Hag da zai ja ragamarta a badi.

Juan Mata

Juan Mata

Asalin hoton, Getty Images

Dan kasar Sifaniya yana daga cikin 'yan wasan farko da kungiyar ta dauko, bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya, David Moyes ne ya kawo shi daga Chelsea a watan Janairun 2014.

Ya kuma yi wa United wasa 285 da cin kwallo 51 da lashe FA Cup da Charity Shield a 2016 da Europa League da League Cup a 2017.

Mai shekara 34 ya buga wasa bakwai a kakar 2021/22 ciki aka fara wasa hudu da shi.

Paul Pogba

Manchester United's Paul Pogba

Asalin hoton, Reuters

Bayan da ya bar Juventus a 2012, Pogba ya sake komawa United a matakin wanda aka saya mafi tsada a duniya kan fam miliyan 89.

Mai shekara 29 dan kwallon tawagar Faransa, wanda karo na biyu da ya koma Old Trafford ya taka rawar gani ya kuma ci karo da kalubale.

Ya taka rawar gani a wata haduwa da United ta doke abokiyar hamayya Manchester City da ci 3-2, daga baya dangantaka ta yi tsami tsakaninsa da Jose Mourinho.

Lokacin da Mourinho ke kociyan United ya karbe mukamin kyaftin ya kuma ce Pogba ba zai sake jan shugabancin 'yan wasa ba.

Dan wasan tawagar Faransa ya bar Old Trafford, wadda ya yi wa wasa 233 da cin kwallo 39 da daukar kofi biyu a 2017.

Jesse Lingard

Jesse Lingard

Asalin hoton, Getty Images

Matashin dan wasa Lingard ya buga wasanni aro a kungiyoyi da yawa, kafin ya samu gurbi a 2015-16, wanda shi ne ya ci kwallon da ya bai wa United damar lashe FA Cup a karawa da Crystal Palace.

Dan wasan ya ci gaba da taka rawar gani a kungiyar ta Old Trafford, kafin daga baya a dai na saka shi a wasanni kamar yadda yake bukata.

Bayan taka leda a wasannin aro a West Ham United a 2020/21, ya koma United har ma ya yi wasa 22 a kakar da aka kammala, zai bar kungiyar bayan yi mata wasa 282 da cin kwallo 35.

Edinson Cavani

Edinson Cavani

Asalin hoton, Getty Images

Dan kasar Uruguay, Cavani ya koma United a cikin watan Oktoban 2020, bayan da yarjejeniyarsa ya karkare a Paris St Germain.

A kakar farko dan wasan mai shekara 35 ya ci kwallo 17 a wasa 39 daga nan ya zura biyu a raga a karawa 20.

Lee Grant

Mai tsaron raga Grant ya koma UUnited daga Stoke City a 2018.

Ya buga wasa biyu, wanda ya sanar a cikin watan Mayu cewar zai yi ritaya a karshen kakar nan, mai shekara 39.

Nemanja Matic

United

Asalin hoton, Clive Brunskill

Dan kasar Serbia yana da sauran kunshin yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar badi, amma cikin watan Afirilu ya sanar cewar zai bar Old Trafford a karshen kakar bana.

Ya koma Old Trafford da taka leda kan fam miliyan 40 a Yulin 2017 a lokacin Jose Mourinho.

Ya buga wasa 189, sai dai bai dauki kofi ba, tun bayan da ya koma United da taka leda.