Robert Lewandowski ya ce zai bar Bayern Munich

An wallafa

Dan kwallon Bayern Munich, Robert Lewandowski ya ce karshen zamansa a Bundesliga ya kare, yana sa ran gwada sa'a a wata kungiyar a kaka mai zuwa.

Lewandowski yana da sauran kwantiragin kaka daya a kungiyar da ke buga Bundesliga, wadda ta lashe kofin kakar nan.

Tun farkon watan nan daraktan wasannin Bayern, Hasan Salihamidzic ya sanar cewar dan wasan mai shekara 33, ya mika bukatarsa ta son barin kungiyar.

Ana ta alakanta Lewandowski da cewar Sifaniya zai koma da taka leda a Barcelona a Camp Nou.

Lewandowski tsohon dan kwallon Borussia Dortmund ya koma Bayern Munich a 2014, kawo yanzu ya lashe Bundesliga takwas da Champions League a 2020.

Ya ci kwallo 50 a wasa 46 a Bayern a bana, ya kuma zura 344 a raga a karawa 375 a kaka takwas da ya yi a Bayern, shi ne na biyu a yawan cin kwallaye a kungiyar, bayan Gerd Muller.