Mohamed Salah ya kara yin karo da cikas a Champions League

An wallafa

Dan kwallon Masar, Mohamed Salah ya kar cin karo da cikas a gasar Champions League, bayan da Real Madrid ta lashe kofin bana da ci 1-0 ranar Asabar a Faransa.

Salah ya ji takaicin abin da ya faru a wasan karshe a gasar Zakarun Turai a 2018, wanda ya fita daga karawar sakamakon rauni da ya ji a kafada, bayan da Sergio Ramos ya yi masa keta.

Daga karshen karawar da suka yi a Ukraine, Real ce ta yi nasara da ci 3-1 ta kuma dauki Champions League na 13 jumulla a tarihi.

Bayan da Liverpool ta doke Villareal ta kai wasan karshe a kofin bana, Salah ya fayyace yadda yake zumudin haduwa da Real Madrid, don huce haushin abin da ya faru a Ukraine.

To sai dai a ranar Asabar Salah ya kara cin karo da cikas a gasar ta Champions League, bayan da Real ta yi nasara da ci 1-0 a Faransa ta dauki kofi na 14 jumulla, Liverpool tana da shida a tarihi.

Salah ya yi iya kokarinsa don ya zura kwallo a raga karo da dama, amma golan Real Madrd, Thibaut Courtois, dan kasar Belgium ya hana kwallayen shiga raga.

Mai tsaron ragar Real Madrid, Courtois shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ke kan gaba a taka rawar gani a fafatawar karshen ta ranar Asabar a Faransa.

Mohamed Salah ya ci karo da koma baya da yawa a kakar nan, bayan da Masar ta kasa lashe kofin nahiyar Afirka a Kamaru, bayan da Senegal ta yi nasara a bugun fenariti.

Haka kuma tawagar Masar ba za ta je gasar kofin duniya da za a yi a Qatar tsakanin Nuwamba zuwa Disamba ba, bayan da Senegal ta kara yi mata fancale.

Sai dai Salah ya kare kakar bana ta Premier League a matakin wanda ke gaba da kwallo 23 a raga, iri daya da yawan na Hueng Son-min na Tottenham da aka raba musu takalmin zinare.

Liverpool wadda ta yi harin lashe kofi hudu a bana ta tsira da Carabo Cup da kuma FA Cup, bayan da Manchester City ta dauki Premier League na kakar nan da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool.

Ranar Asabar kuma Real Madrid ta ci Champions League a kan Liverpool na 14 da ta dauka a tarihi.