Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real za ta buga wasan karshe a La Liga da Betis a gida
Real Madrid za ta buga wasan karshe a kakar bana a La Liga, karawar mako na 38 a Santiago Bernabue, inda za ta karbi bakuncin Real Betis ranar Juma'a.
Real wadda ta lashe La Liga na bana na 35 jumulla na fatan cin wasan a gaban 'yan kallonta a shirin da take na buga karawar karshe a Champions League da Liverpool ranar 28 ga watan Matu a Faransa.
Cikin fafatawar da Real Madrid ta yi a Santiago Bernabeu a La Liga ta bana ta yi nasara a wasa 13 da canjaras hudu aka doke ta daya, shi ne na El Clasico da Barca ta ci.
Real Madrid ce kan gaba a sharara kwallaye a kakar nan a babbar gasar tamaula ta Sifaniya da 80, kuma Karim Benzema ne kan gaba a yawan cin kwallaye a kungiyar.
Kawo yanzu dan kwallon tawagar Faransa ya zura 27 a raga a La Liga, shi ne zai lashe takalmin zinare a matakin wanda ke kan gaba a cin kwallaye a gasar a kakar nan.
Real Betis za ta ziyarci Real Madrid da kwarin gwiwa, bayan da take ta biyar a kan teburi, kuma ita ta lashe Copa del Rey na bana.
Kawo yanzu Betis ta yi nasara a wasa 19 a La Liga ta bana da canjaras bakwai aka doke ta wasa 11, kuma ta ci wasa biyu a jere kwanan nan a fafatawa da Valencia da kuma Granada.
'Yan wasan Betis Juanmi ya ci kwallo 16 a gasar La Liga da kuma Borja Iglesias da ya zura 10 a raga a kakar bana.
'Yan wasan Real Madrid da za su kara da Real Betis:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin, Fuidias.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Vallejo, Nacho, Marcelo, F. Mendy.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Isco, Camavinga.
Masu cin kwallaye: Hazard, Benzema, Asensio, Jović, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.