Xavi bai yi rashin nasara a wasannin waje a La Liga a Barca ba

An wallafa

Ranar Lahadi Barcelona za ta buga wasan karshe a gasar La Liga ta bana a Camp Nou karawar mako na 38 da Villareal.

Ranar Lahadi Barcelona ta tashi 0-0 a gidan Getafe a wasan mako na 37 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya, shi ne na karshe da ta fafata a bana a waje a La Liga.

Tun bayan da Xavi Hernandez ya karbi aikin horar da Barcelona ranar 6 ga watan Nuwamba, bai yi rashin nasara ba a karawar waje da ya yi a La Liga ta kakar nan.

Kociyan wanda ya maye gurbin Ronald Koeman, ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta karkare a karshen watan Yunin 2024.

Kawo yanzu Xavi ya ci wasa tara da canjaras biyar a fafatawa 14 da jan ragamar Barcelona a wasannin da ta yi a waje a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Kungiyoyin da ya doke a waje sun hada da Betis, Real Sociedad, Levante, Elche, Valencia, Alavés, Mallorca, Villarreal da kuma Real Madrid.

Kungiyoyin da Xavi ya yi canjaras da su ba a Camp Nou ba a La Liga sun hada da Getafe, Espanyol, Granada, Sevilla da kuma Osasuna.

Da wannan bajintar, Xavi ya zama na uku da ya ja ragamar wasa a kalla 10 ba tare da rashin naasara ba a waje, bayan Ernesto Valverde mai 12 da canjaras shida, sai kuma Tito Vilanova mai 10.

Tun da aka fara kakar bana, Barcelona ta sha kashi a wasa biyu kacal a waje wato 2-0 a gidan Atletico Madrid da kuma 1-0 a Rayo Vallencano.

Kuma tun kan Xavi ya koma Barcelona da horar da tamaula, kungiyar ta Camp Nou ta yi canjaras da Celta, Cádiz da kuma Athletic Club.