Liverpool ta lashe kofin FA bayan doke Chelsea

An wallafa

Liverpool ta lashe kofin FA bayan ta doke Chelsea a bugun fanariti.

Liverpool ta yi nasara ne da ci 6-5 a fanariti bayan an kammala lokacin wasan da ƙarin lokaci babu ci.

Yanzu Liverpool ta haɗa kofi biyu a kakar bana, kuma tana harin lashe kofin Zakarun Turai da na Premier a makwanni masu zuwa. Ko da yake maki uku Manchester City ta ba Liverpool a teburin Premier.

Liverpool za ta iya kafa tairihi idan ta lashe kofuna huɗu a kaka ɗaya.

Wannan ne karon farko da aka buga wasan ƙarshe tare da ƴan kallo a gasar FA a filin wasa na Wembley tun 2019 saboda annobar korona.

Cesar Azpilicueta da Mason Mount suka ɓarar wa Chelsea da ƙwallaye biyu a bugun fanariti yayin da Sadio Mane ya ɓarar wa Liverpool ƙwallo ɗaya.

Wannan ne karon farko da Jurgen Klopp ya lashe kofin FA, kuma karon farko da Liverpool ta ɗauki kofin tun 2006.

Karon farko kenan da Liverpool ta lashe kofi biyu na cikin gida a kaka ɗaya tun kakar 2000-01