Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Lingerd, Lewin, Rice, Phillips, Lukaku, Sterling da De jong

An wallafa

Newcastle za ta yi tayin siyan dan wasan Everton da Ingila Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 25 a bazara. Sun dade suna sha'awar dan wasan da ita ma Arsenal ke fakonsa.(Telegraph)

Bayern Munich ta shiga zawarcin dan wasan United Paul Pogba, inda tuni Juventus da Paris St-Germain da Real Madrid da kuma Manchester City ke farautar dan wasan na Faransa mai shekara 29. (Fichajes)

Robert Lewandowski, mai shekara 33, ba zai rattaba hannu kan sabon kwantaragi a Bayern Munich ba, kuma ana iya siyar da dan wasan gaban na Poland ga Barcelona a bazara kafin ya shiga shekarar karshe ta kwantiraginsa. (Goal)

Chelsea na son kammala siyan dan wasan bayan Sevilla da Faransa Jules Kounde, mai shekara 23, a farkon lokacin bazara. (Give Me Sport)

Dan wasan tsakiyar Manchester City da Ingila Raheem Sterling, mai shekara 27 na tsammanin zai koma daya daga cikin manyan kungiyoyin Turai idan ya bar Etihad a bazara. Arsenal da Tottenham na cikin masu tsananin sha'awarsa. (The Athletic)

West Ham ba za ta ci gaba da tattaunawa da dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice ba har sai an rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara bayan dan wasan mai shekara 23 ya ki amincewa da kwantiragin shekara takwas na fam miliyan 83. (Sky Sports)

Aston Villa na zawarcin dan wasan tsakiyar Leeds da Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26. (Insider Football).

Manchester United na sa ido kan halin da dan wasan Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong ke ciki a Nou Camp, Barca dai ta yi masa kudi a kan fam miliyan 70, sai dai mai shekara 25 din ya fi son komawa kungiyar da za ta buga gasar zakarun Turai. (Mails)

Kocin West Ham David Moyes yana son hada Phillips da dan wasan tsakiya na Ingila Rice a filin wasa na Landan. (Sun)

Idan Barca ta yi rashin De Jong a bazara, kociyanta Xavi zai nemi ya maye gurbinsa da dan wasan tsakiya na Manchester City da Portugal Bernardo Silva, mai shekara 27. (Mundo Deportivo)

Dan wasan gaban Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 28, yana son ci gaba da zama a Chelsea a bazarar nan duk da rashin jin dadin da yake yi a Stamford Bridge (Give Me Sport)

Dan wasan gefe na Arsenal Reiss Nelson, mai shekara 22, zai tattauna da Mikel Arteta game da makomarsa bayan tafiya aro na tsawon shekara daya a Feyenoord.

Wasu kungiyoyin gasar Premier suna zawarcin dan wasan na Ingila, amma Gunners na ci gaba da nuna tana son abinta. (Fabrizio Romano)

Kocin Aston Villa Steven Gerrard na neman dan wasan bayan Liverpool da Ingila Joe Gomez, mai shekara 24 a bazara. (Mirror)

West Ham na ci gaba da sha'awar sayen dan wasan gaban Manchester United da Ingila Jesse Lingard, mai shekara 29, wanda ya shafe kakar wasa a matsayin aro tare da Hammers kuma kwantiraginsa zai kare a bazara. (90Mint)