Karim Benzema ya yi kan-kan-kan da Robert Lewandowski a cin kwallaye

An wallafa

Ranar Laraba Real Madrid ta yi nasara a kan Manchester City da ci 3-1 a wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da suka fafata a Santiago Bernabeu.

Rodrygo ne ya ci wa Real kwallo biyu daga baya Karim Benzema ya ci na uku a bugun fenariti kuma na 86 da ya sharara a raga a gasar Zakarun Turai.

Real Madrid ta kai wasan karshe da cin kwallaye 6-5 gida da waje da suka fafata - za kuma ta kara da Liverpool a Faransa a ranar 28 ga watan Mayu.

Kawo yanzu Benzema ya yi kan-kan-kan da Lewandowski a mataki na uku a jerin wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a tarihin gasar.

Cristiano Ronaldo ne na daya mai kwallo 141 a raga, sannan Lionel Messi mai 125 a wasannin da ya yi a Barcelona da Paris St Germain.

A kakar nan ta bana dan wasan tawagar Faransa ya ci 15 a gasar Zakarun Turai ta Champions League da hakan ya sa Real Madrid ta kai karawar karshe.

Benzema ya fara da zura kwallo biyar a wasannin cikin rukuni a kakar nan, daga nan ya ci 10 a zagayen gaba da na rukunnai.

Haka kuma dan wasan ya ci kwallo a kowacce kakar Champions League 17 a jere ba fashin zura su a raga.

Ya kuma fara cin kwallo a Champions League a 2005-06 a karawa da Rosenborg a lokacin da yake taka leda a Olympique Lyon, wadda yake da 12 jumulla kan ya bar kungiyar.

Sauran 74 ya ci ne a Real Madrid - ya kuma fara a kungiyar Sifaniya ranar 3 ga Nuwambar 2009 a fafatawa da Milan.

Kungiyoyin da Benzema ya ci kwallaye da yawa sun hada da Galatasaray da PSG da kuma Chelsea, wadanda ya ci biyar-biyar kowacce.