Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Liverpool za ta iya lashe kofi hudu a bana?
Liverpool na kan hanyar lashe kofi hudu - tarihin da ba a taɓa yi ba a Ingila.
Wasanni shida suka rage wa Liverpool ta kafa wannan tarihin na lashe kofuna huɗu a kaka ɗaya.
Liverpool za ta iya lashe kofi huɗu a kakar bana - ko kuma ta ƙare da kofi ɗaya kacal na Carabao da ta lashe.
Celtic ce kawai a kakar 1966-67 ta lashe kofin Turai da lig da kuma kofin ƙalubale na gida - ko da yake yawancin ƙasashen ba a buga gasa biyu a cikin gida a kaka ɗaya.
Liverpool yanzu ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai - za ta haɗu ne da Real Madrid ko Manchester City a Paris.
Maki ɗaya ya raba Liverpool tsakaninta da Manchester City da ke jagorancin teburin Firimiya, yayin da ya rage wasanni huɗu a kammala gasar.
Nasarar da Liverpool ta samu kan Villarreal a gasar Zakarun Turai a ranar Talata na nufin:
- Liverpool ita ce ƙungiya ta farko a Ingila da ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai da FA da kuma lig na cikin gida.
- Liverpool ta lashe kofin Carabao kuma za ta kai wasan ƙarshe a gasar Zakarun Turai da kuma gasar FA
- Za ta kasance ƙungiya ta farko da ta lashe kofi huɗu na Zakarun Turai da Firimiya da FA da kuma Carabao
Kofi huɗu - me zai hana? In ji Salah
Liverpool ta lashe kofi uku tun da ta ɗauko Mohamed Salah a 2017 - Kofin Zakarun Turai a kakar 2018-19 da Firimiya a 2019-20 da Carabao a bana.
Kofi uku kawai ta lashe a shekara 13 kafin zuwansa.
Ɗan wasan na Masar wanda shi ya fi ci mata ƙwallaye a raga a kakar bana da ƙwallaye 30 ya ce: "Muna yaƙin lashe komi. Mun ɗauki kofi ɗaya kuma yanzu mun kai wasan ƙarshe. Za mu ci gaba da yaƙi a Firimiya.
"Kofi huɗu muka sa a gaba a yanzu, Kila ba tun da aka soma kaka ba. Na fi mayar da hankali kan kofin Zakarun Turai da na Firimiya. Amma yanzu me zai hana? Bayan mun doke Man City a FA wasan dab da ƙarshe ina ganin hakan na iya faruwa.
"Bayan wasannin rukuni, na fara tunanin, za mu lashe kofin Zakarun Turai a bana."
"Na fi son mu buga wasan ƙarshe da Madrid. City ba sauki."
Klopp ya ƙara da cewa "abu ne mai wahala ka iya kai wasan ƙarshe a gasa uku, kila shi ya sa babu wanda ya taɓa yi."