Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Rice, Martinez, Traore, Aarons, Ebiowei da Bergwijn
Manchester United za ta samu damar sayen dan wasan tsakiya na Ingila Declan Rice, mai shekara 23, daga West Ham, yayin da abokan hamayyarta su ma za su mayar da hankali wajen karfafa wasu fannoni. (ESPN)
Everton za ta karɓi fan miliyan 50 kan dan wasan gaban Brazil Richarlison, mai shekara 24, a wannan bazarar kuma tana da kwarin gwiwar samun irin wannan tayin. (Football Insider)
AC Milan da Juventus ne ke kan gaba wajen neman dan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Jesse Lingard, mai shekara 29. (ESPN)
Arsenal ta sake sabunta zawarcin dan wasan gaban Inter Milan da Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 24. (Times)
Dan wasan tsakiya na RB Leipzig da Austria Konrad Laimer, mai shekara 24 na jan hankalin ƙungiyoyi kamar Tottenham da Liverpool, da kuma Bayern Munich waɗanda dukkansu ke zawarcinsa. (Kicker)
Ana raɗe-raɗin komawar ɗan wasan Lazio da Serbia Sergej Milinkovic-Savic, mai shekara 27 Manchester United ko Paris St-Germain. (90Mint)
Leeds ba za ta yi wa dan wasan tsakiyar Ingila Kalvin Phillips, mai shekara 26, sabon tayin kwantiragi ba har sai watan Yuni. (Star)
Ajax za ta sake farfado da sha'awarta, ta na neman dan wasan Tottenham da Netherlands Steven Bergwijn bayan dan wasan mai shekaru 24 ya ce a shirye yake ya bar kungiyar. (Times)
Dan wasan bayan Newcastle na Ingila Paul Dummett, mai shekara 30, na shirin kulla sabuwar yarjejeniya a kulob din. (Sun)
Barcelona ba za ta sayi dan wasan gaban Wolves Adama Traore, mai shekara 26, a matsayin dindindin a bazara ba. A halin yanzu dan wasan na Spain yana zaman aro ne a kungiyar ta La Liga. (Marca)
Norwich da ta koma matakita na farko na shirin siyar da tsohon dan wasan bayanta ɗan Ingila Max Aarons, mai shekara 22, a bazarar nan. (Telegraph)
Tottenham da Leeds da Fulham na zawarcin tsohon dan wasan gaban Ingila na 'yan kasa da shekara 16, Malcolm Ebiowei, mai shekara 18. (Sun)
Fulham da ke shirin ɗagowa zuwa babbar gasar Premier ta tuntubi dan wasan Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 23, daga Coventry City. (Fottball Insider)