Real Madrid ta lashe gasar La Liga karo na 35

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid ta lashe babbar gasar La Liga ta Spaniya karo na 35 a tarihi.
Real ta cimma wannan tarihi ne bayan doke Espanyol 4-0 a yammacin Asabar a filin wasa na Santiago Bernabéu.
An sallama wa Real kofin ne duk da cewa saura wasa huɗu a kammala gasar.
Daga cikin wasannin da suka rage wa Real har da na hamayar birnin Madrid tsakaninta da Atletico. Sauran su ne Levente da Cadiz da Real Betis.

Asalin hoton, Getty Images
Hakan na nufin mai horarwa Carlo Ancelotti ya kafa tarihi a matsayin koci ɗaya tilo da ya lashe gasar league a manyan ƙasashen Turai biyar.
Ya ci gasar Serie A a AC Milan, da Ligue 1 a PSG, da Premier League a Chelsea, da kuma Bundesliga a ƙungiyar Bayern Munich.
Ƙwallaye biyu da matashin ɗan wasa Rodrygo ya ci, da ƙwallon Asensio, da kuma ta zaƙaƙuri Benzema su ne suka bai wa Real Madrid nasara.
Da ma tun kafin wasan, Madrid na neman maki ɗaya ne kacal ta jinjina kofin.
Yanzu kokawa ta rage tsakanin Seviila (ta biyu a teburi) da Barcelona (ta uku) da Atletico Madrid (ta huɗu) da Real Betis (ta biyar) da Real Sociedad (ta shida) da Villarreal (ta bakwai), waɗanda dukkansu ke da damar zuwa gasar Zakarun Turai ta Champions League a baɗi.










