Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ralf Rangnick: Kocin Manchester United na riƙon ƙwarya zai karɓi aikin horar da Austria
An bayyana kocin riƙon ƙwarya na Manchester United Ralf Rangnick a matsayin kocin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Austria.
Duk da haka Rangnick zai karɓi muƙaminsa na mai ba da shawara a ƙarshen kakar nan a Man United kamar yadda aka tsara.
"Na zaƙu na ba da gudummawata wajen dawo da kimar United," a cewarsa.
Ɗan ƙasar Jamus ɗin mai shekara 63 ya saka hannu kan yarjejeniyar shekara biyu da Austria kuma zai fara aikin ne bayan kammala gasar Premier League a watan Mayu mai zuwa.
"Girmamawa ce a gare ni na sake zama mai horarwa," in ji shi.
"Hangen lashe Gasar Turai a Jamus tare da matashiyar tawaga da ke son samun nasarori na sa ni yin hasashe sosai."
Austria wadda take matsayi na 23 a jerin ƙasashen ƙwallon ƙafa na Fifa, ta kasance ba tare da mai horarwa ba tun bayan da Franco Foda ya yi ritaya a watan Maris bayan sun gaza samun gurbin shiga gasar Kofin Duniya na wannan shekarar.
"Muna murna sosai da samun ƙwararre a harkar ƙwallonn ƙafa ta ƙasa da ƙasa a matsayin koci," kamar yadda shugaban hukumar ƙallon Austria, Gerhard Milletich ya bayyaana.
Man United ta ci wasanta 10 cikiin 25 a dukkan gasa tun bayan da Rangnick ya maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a watan Nuwamba.
Yanzu haka United na mataki na 6 da maki 55 kuma babu tabbas ko za ta ƙare kakar bana cikin 'yan huɗun farko da za su buga gasar Zakarun Turai ta Champions League.