Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Karim Benzema ya buga wa Real Madrid wasa na 600 a Etihad
Manchester City ta yi nasarar doke Real Madrid da ci 4-3 a wasan daf da karshe a Champions League ranar Talata a Etihad.
Karim Benzema ya buga wasan, shi ne ya ci wa Real Madrid kwallo biyu a karawar zangon farko a daf da karshe a gasar bana.
Kawo yanzu Benzema ya yi kan-kan-kan da Gento a yawan yi wa Real wasanni, saura daya ya tarar da Fernando Hierro mai 601 a kungiyar.
Dan kwallon tawagar Faransa ya zama na takwas a jerin wadanda suka yi wa Reak Madrid karawa da mai yawa, idan ka cire Raúl mai wasa 741.
Sauran sun hada da Casillas mai wasa 725 da Sanchís mai 710 da Sergio Ramos mai 671 da kuma Santillana mai wasa 645 da ya yi wa Real Madrid.
Benzema ya dauki kofi 20 a Real, ciki har da Champions Leagues hudu da Club World Cups hudu da kuma UEFA Super Cups.
Sauran sun hada da LaLiga uku da Copas del Rey da Spanish Super Cups hudu.