Champions League: Liverpool da Villareal a Anfield

An wallafa

Liverpool ta karbi bakuncin Villareal da za su kara a wasan farko a daf da karshe a Champions League ranar Laraba a Anfield.

Liverpool ta kawo wannan matakin, bayan da ta fitar da Benfica, ita kuwa Villareal Bayern Munich ta casa a kakar bana.

Liverpool mai fatan lashe kofi hudu a bana, bayan da ta dauki Caraboa Cup tana ta biyu a teburin Premier League da tazarar maki daya tsakaninta da Manchester City mai jan ragama.

Villareal mai rike da Europa League tana da maki 52 a mataki ta bakwai a kan teburin La Liga na bana.

Wannan shi ne karo na uku a kaka biyar da Klopp ya kai Liverpool wasannin daf da karshe a babbar gasar tamaula ta Zakarun Turai.

Klopp ya yi rashin nasara a hannun kocin Villareal, Unai Emery a lokacin da yake jan ragamar Sevilla a 2015-16 a gasar Europa League kakar farko a Liverpool da kocin Jamus ya fara aiki.

Sai dai kuma Liverpool ta kai wasan karshe a Champions League sau biyu a jere, wadda ta lashe kofin 2019.

Liverpool tana da Champions League shida jumulla.

Wasa biyu da kungiyoyin suka kara a tsakaninsu:

Europa League Alhamis 5 ga watan Mayun 2016

  • Liverpool 3 - 0 Villarreal

Europa League Alhamis 28 ga watan Afirilun 2016

  • Villarreal 1 - 0 Liverpool