Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester United 3-2 Norwich City: 'Muhimmancin Ronaldo ga Man Utd ba zai misaltu ba'
- Marubuci, Daga Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport at Old Trafford
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 2
Shin Cristiano Ronaldo shi ne silar matsalolin Manchester United ko kuwa shi ne maganin matsalolin kungiyar? Wannan ita ce tambayar da ake ta yi a Old Trafford.
Kwallaye uku masu ban-mamaki da Ronaldo ya zura - lamarin da ya sa suka tashi da ci 3-2 a gida a fafatawarsu da Norwich ranar Asabar ta bai wa kungiyar kwarin gwiwar samun gurbi a Gasar Zakarun Turai ta kaka mai zuwa.
Rawar da ya taka ta sa dan kasAr ta Portugal ya kai ga zura kwallo 99 a Gasar Firimiya sannan ya zama na uku, da hadin gwiwar wasu 'yan wasan, a matsayin wanda ya fi zura kwallo a Gasar Firimiya ta bana inda ya ci kwallo 15.
Wannan ita ce kaka ta 16 a jere da Ronaldo ya ci kwallo 20 zuwa sama a dukkan gasa, kuma ya zarta kowanne dan wasan United da kwallo 12 a bana.
Tabbas wadannan alkaluma ne da za su sa mutane su yi ta magana kan dan wasan mai shekara 37? Kamar yadda kocin Norwich Dean Smith ya tabbatar.
"Na shaida wa 'yan wasana cewa a yayin hutun rabin-lokaci idan kuka ci min kwallo 20 sannan kuka taimaka aka ci kwallo 15, ba sai kun jajirce ba," in ji shi.
Abin da hakan ke nufi shi ne, idan dai Ronaldo zai ci gaba da zura kwallaye, bai kamata United ta raba-gari da shi ba.
Kuma a halin yanzu, kwallayen da yake zurawa su ne suke fitar da Old Trafford daga kunya.
Idan aka hada da kwallo uku da ya ci a karawarsu da Tottenham wasanni biyu da suka gabata, Ronaldo ne dan wasan daya tilo da ya zura wa United kwallaye a Gasar Firimiya da aka saka shi a ciki tun wasan da suka doke Leeds ranar 20 ga watan Fabrairu.
Zai ci gaba da zama mai muhimmanci ga tawagar United, kuma idan Erik ten Hag ya zama kocin kungiyar kamar yadda aka yi hasashe, dole a tattauna kan ko Ronaldo zai ci gaba da zama a Old Trafford a shekarar karshe ta kwangilarsa.
"Wannan ba abin da zan yanke hukunci a kai ba ne,"a cewar kocin rikon-kwarya na United Ralf Rangnick. "Cristiano yana da sauran shekara daya a kwangilarsa. Wannan batu ne da sabon koci zai yanke hukunci a kansa tare da hukumar gudanarwar kungiyar.