Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan wasan Real Madrid da za su kara da Getafe a La Liga
Real Madrid za ta karbi bakuncin Getafe a wasan mako na 31 a gasar La Liga da za su kara ranar Asabar a Santiago Bernabeu.
Kungiyoyin sun fafata ranar 2 ga watan Janairun 2022 a gasar La Liga, inda Getafe ta yi nasara da ci 1-0, kuma Enes Unal ne ya ci mata kwallon a minti na tara da fara wasan.
Real Madrid tana ta daya a kan teburin La Liga da maki 69, bayan da Seville wadda take biye da ita keda maki 60, sai Barcelona mai kwantan wasa ta uku mai maki 57.
Ita kuwa Getafe mai maki 32 tana ta 14 a kasan teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Tuni Carlo Ancelotti ya bayyana 'yan wasan da zai fuskanci Getafe da su.
'Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Diego.
Masu tsaron baya: Carvajal, E. Militão, Alaba, Nacho da kuma Marcelo.
Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos da kuma Camavinga.
Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Bale, Vini Jr., Rodrygo da kuma Mariano.