Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ba a doke Real Madrid idan Bale ya ci mata kwallo
A ranar Asabar Real Madrid ta doke Huesca da ci daya mai ban haushi a gasar La Liga wasan mako na 15, kuma Gareth Bale ne ya ci kwallon.
Jumulla Bale ya ci wa Real kwallo bakwai a kakar bana kenan, kuma idan ya zura a ragar abokiyar hamayya, ba a doke Madrid a wasan sai dai ta hada maki uku a karawar.
Bale ya fara ci wa Real Madrid kwallo a gasar La Liga shekarar nan a karawar da ta yi da Getafe, ya kuma ci Girona da Leganés.
Dan wasan tawagar Wales ya kara ci wa Madrid kwallo a gasar Zakarun Turai ta Champions Legue a karawar da Real ta yi da Roma a Bernabeu.
Haka kuma ya ci Viktoria Plzen, sannan ya kara zura kwallo a Italiya a karawa da Roma a dai gasar ta Zakarun Turai.
Bale din shi ne na biyu a yawan ci wa Real kwallo a bana da bakwai a raga, biye da Karim Benzema wanda ya ci 10 jumulla a kakar shekarar nan.