Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An dakatar da haska wasannin Premier Rasha
Hukumar shirya gasar Premier ta dakatar da yarjejeniyarta da Rasha na haska gasar sakamakon mamayar da Rashan ta yi wa Ukrain me makwabtaka da ita.
Wannan mataki zai fara aiki ne nan take, wanda hakan ke nufin ba za a haska wasanni hudun da za a yi ba a gasar ranar Alhamis.
An yanke hukuncin ne cikin minti 15 na tattaunawar da aka yi ta sa a hudu da rabi da duka kungiyoyin gasar 20 a Landan a ranar Talata.
Za a bayar da taimakon fan miliyan daya domin taimakawa mutanen Ukrain.
Wani kamfani da ake kira Rambler ne ke da lasisin haska gasar Premier a Rashan. A yanzu haka kuma yarjejeniyar sa da hukumar gasar na shekarar ta ta karshe.
A wani matakin kuma na daban, hukumar FA itama ta soke yarjejeniyarta da Rasha.
Hakan na nufin babu ko wasa guda daga cikin na kusa da karshe da za a yi a gasar FA da za a haska.
Premier ta yi Allah-wadai da mamayar da Rasha ta yi wa Ukrain kuma duka kungiyoyin gasar sun amince da wannan mataki.
"Muna kiran a samu zaman lafiya kuma muna fatan wadan nan matakai da muke dauka za su yi tasiri," hukumar gasar ta sanar.
"Hukumar ba da agajin gaggawa za a bai wa fan miliyan dayan domin raba kayan agaji ga mabukata."
A makon jiya, kungiyoyin Premier sun nuna goyon baya ga Ukrain ta hanyar daura kambu mai launin tutar kasar, yayin da aka rika sanya tutar kasar a ko ina a cikin filayen wasa.
Wannan mataki na da alaka da kin haska wasannin Premier da China ta yi a makon jiya.
China dai na da alakar siyasa ta kud-da-kud da Rasha.