Clarence Seedorf: Tsohon dan kwallon Holland ya Musulunta

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Holland Clarence Seedorf ya musulunta, kamar yadda ya sanar a shafinsa na Instagram.

Tsohon ɗan ƙwallon na Ajax da Real Madrid da AC Milan wanda ya lashe kofin zakarun turai sau huɗu ya ce matarsa ce ta musuluntar da shi tare da koyar da shi addinin Islama.

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na Instgram inda yake tabbatar musuluntarsa, Seedorf ya bayyana godiya ga matarsa da kuma waɗanda suka tura masa sakwannin murna na shiga addinin musulunci.

"Ina matuƙar cikin farin ciki da kuma farin cikin kasancewa dukkan 'yan uwa a fadin duniya musamman masoyiyata Sophia wadda ta karantar da ni ma'anar Musulunci," kamar yadda Seedorf ya bayyana a shafinsa na Instagram.

Sai dai tsohon fitaccen ɗan wasan ya ce ba zai sauya sunansa ba, duk da ya musulunta yana mai cewa zai ci gaba da amfani da sunansa na Clarence Seedorf.

"Ban sauya sunana ba kuma zan ci gaba da amfani da Clarence Seedorf suka raɗa min!"

Matarsa, Sophia Makramati, ƴar Canada ce asalin Iran kuma sun shafe shekara biyu a Dubai, Daular Larabawa.

Ta bayyana farin cikinta a Instagram da kuma rawar da ta taka ga musuluntar da Seedorf.

"Ina matuƙar farin ciki da alfahari da kasancewa cikin wannan muhimmin lokaci na soyayyata da Clarence Seedorf na shiga cikin al'ummar Musulmi," in ji ta.

Sama da mutum 34,000 suka yi tsokaci a saƙon na Seedorf a Instagram yayin da mutum 376,000 suka so saƙon.

Seedorf yana cikin ƴan wasan da suka yi tashe a ƙwallon ƙafa da ke magana da harsuna da dama na duniya, harshen Holand da Inglishi da na Italiya da Spain da fotuganci da na Tongo.

Tsohon ɗan ƙwallon ya lashe kofin zakarun Turai a Ajax a 1995 da Real Madrid a 1998 da 2003 da kuma 2007 a AC Milan. Ya kuma lashe La liga a Real Madrid a 1997 da kofin Seria biyu a AC Milan a shekarun 2004 da 2011.

Ya taɓa horar da ƴan wasan Kasar Kamaru kafin sallamar shi bayan gasar cin kofin Afirka a 2019