Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Pogba, Wijnaldum, Haaland, Onana, Christensen, Diaby, Kepa, Saka

An wallafa

Juventus ta tuntubi wakilin Paul Pogba kan yiwuwar ya koma taka mata leda idan wa'adin kwantiraginsa ya kawo karshe a Manchester United a karshen kaka. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Albashin Pogba zai ragu idan ya amince ya koma Juve, wanda ke da jan aiki wajen iya shawo kan ɗan wasan da ya lashe kofin duniya ya koma gareta ganin akwai kungiyoyi irinsu Paris St-Germain da Real Madrid na zawarcinsa, Pogba ɗan Faransa ne mai shekara 28. (Calciomercato - in Italian)

West Ham ta nuna zaƙuwa kan saye ɗan wasan Belgium mai buga tsakiya Amadou Onana daga Lille, wanda ke son ake biyansa sama da £20m. (Sun on Sunday)

Atletico Madrid na duba yiwuwar sayo ɗan wasa daga Paris St-Germain mai shekara 31 Gini Wijnaldum, wanda ke nazarin makomarsa kasa da shekara guda da cimma yarjejeniyar shekara uku da ƙungiyarsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Ɗan wasanChelsea Andreas Christensen mai shekara 25, yaƙi amincewa da tayin da ƙungiyoyin Firimiyar Ingila suka gabatar a kansa kuma yana gab da amincewa da tayin Barcelona, wadda tayin ta ya fi na Bayern Munich gwaɓi. (Fabrizio Romano)

KocinBarcelona Xavi Hernandez ya ce yana da kwarin-gwiwar kungiyarsa za ta yi nasara a farautar saye ɗan wasan Borussia Dortmund mai shekara 21 Erling Braut Haaland. (Sun on Sunday)

Mai horas da Lazio Maurizio Sarri ya zaƙu ya sake kasancewa da mai tsaron ragar Chelsea mai shekara 27 Kepa Arrizabalaga na Rome, tsohon kocin na Chelsea na harin dan wasan ne ya zo musu a matsayin ɗan aro. (Corriere dello Sport - in Italian)

Leeds na iya kwada sa'arta kan ɗan wasan Manchester United mai shekara 20 James Garner a sabon kaka, yayinda Southampton ta kwadaitu da ɗan wasan na Ingila da ke zaman aro a Nottingham Forest. (Sun on Sunday)

Arsenal da Newcastle United na zawarci ɗan wasan Sevilla mai shekara 24 Youssef En-Nesyri na Moroko, a watan Janairu an yi ta alakanta ɗan wasan da Manchester United.(Teamtalk)

Ɗan wasan Ingila mai buga tsakiya Bukayo Saka ba shi da burin barin Arsenal, duk da zarwacin da Liverpool ke nunawa kan ɗan wasan mai shekara 20. (Sun on Sunday)

Alexander Isak na Real Sociedad da ɗan wasan Everton Dominic Calvert-Lewin sun kasance 'yan wasan da rade-radi ke cewa Arsenal na farauta bayan kocin Gunners Mikel Arteta ya ce 'yan wasan da ke kai hari zai fi mayar da hankali wajen sayawo a sabuwar kaka. (Sunday Express)

Bayer Leverkusen za ta buƙaci kudaden da yawansu ya kai euro miliyan 100 kan ɗan wasanta mai shekara 22 Moussa Diaby, da Newcastleke zawarci.(Sport Witness)

Crystal Palace ta shiga sahun su Manchester United, Newcastle daWest Ham da le farautar Boubacar Kamara daga Marseille. (Sun on Sunday)

Ɗan wasan Wales Joe Rodon na duba yiwuwar bankwana da Tottenham a wannan kakar. (Football Insider)

Ana alakanta ɗan wasan Jamhuriyar Czech Alex Kral da kulob din da ke buga league na daya Montpellier a sabuwar kaka. (Foot Mercato - in French)