Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mbappe ya ce bai yanke shawarar inda zai tafi ba
Kylian Mbappe ya ce har yanzu bai yanke shawarar ƙungiyar da zai koma nan gaba ba daga Paris St-Germain, bayan da ya ci kwallo daya tilo a karawarsu da Real Madrid ta farko, zagayen kungiyoyi 16 a Paris.
Ana dai danganta Mbappe da tafiya Real Madrid idan kwantiraginsa ya kare a lokacin bazara.
A hirarsa da tashar talabijin ta Movistar TV, Mbappe ya bayyana cewa, ''Ina yi wa daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a duniya wasa.
Zan yi mata duk abin da zan iya a sauran lokacin da ya rage na kakar nan. Ban yanke shawara a kan makomata ba,'' in ji shi
An dauki karawar ta ranar Talata kamar wani gwaji da Real Madrid, wadda ta nace sai ta ɗauko Mbappe, ta yi masa to amma ana ganin ko hakan ne ko ba hakan ba ne, ya dai nuna kansa a wasan.
Dan Faransar mai shekara 23, shi ne ya kai hari daya tilo na PSG a kashin farko na wasan, ya kuma samu fanareti a minti na 62, lokacin da aka yi masa keta, sai dai kuma Lionel Messi ya barar da fanaretin.
Da sakamakon wasan na Talata Madrid na bukatar kwallo biyu a karawa ta biyu da za su yi a gidanta, Bernabeau a wata mai zuwa kafin ta ga bayan PSG.
Ana ganin dan wasan ya bari ne har sai bazara lokacin da kwantiragin nasa zai kare kafin ya yanke shawarar inda zai koma.
Dan jarida Julien Laurens ya ce, ''Abin ban sha'awa ne da jan hankali ganin yadda baya son bayyana matsayinsa kafin karawarsu ta biyu,''
Laurens ya ce, yana ganin zai bari ne har zuwa karshen kaka, inda zai iya tafiya duk inda ya ga dama lokacin ba wani kwantiragi a kansa.