Afcon 2021: Vincent Aboubakar dan wasan da ya fi cin kwallo a raga

An wallafa

Vincent Aboubakar na fatan dacewa da takalmin zinari a matsayin wanda ya fi cin ƙwallaye a gasar cin kofin Afirka a Kamaru

Kaftin ɗin na Kamaru ya zura kwallo a dukkanin kasashen da Kamaru ta hadu da su a gasar cin kofin Afirka da ake gudanarwa a ƙasarsa.

Ya haɗa ƙwallaye shida kawo yanzu tun soma gasar, kuma ya kafa tarihin da Samuel Eto'o ya kafa na cin ƙwallaye biyar lokaci guda a wasannin Kamaru.

Dan wasan ya ci Burkina Faso da Ethiopia da Cape Varde a wasannin rukuni, kafin ya ci Comoros a zagaye na biyu.

Wane ne Vincent Aboubakar?

Vincent Aboubakar a 2010 ya fara buga wa ƙasarsa Kamaru wasa, kuma ya yi haskawa 80.

A ranar 11 ga watan Agustan 2010 ya fara ci wa Kamaru kwallo a raga a wasan sada zumunci da Poland.

Vincent Aboubakar mai shekara 30 ya ci wa Kamaru ƙwallaye jimilla 31 a haskwa 81.

Aboubakar shi ne kaftin ɗin Kamaru, kuma yana taka leda ne a Saudiyya a kulub din Al Nassr.

Ya fara rayuwar tamaula ne a kulub din Coton Sport kafin ya tsallaka Turai a 2010.

Ya fara taka leda a Faransa a Valenciennes kafin ya koma Lorient inda ya ci kwallaye 26 a haskawa 109.

A 2014 ya koma FC Porto a Portugal inda ya ci ƙwallaye 58 a haskawa 125, tare da ɗaukar kofin Lig na ƙasar.

Ya ci Super Lig a Besktas ta Turkiya a 2017 da 2021 a matsayin ɗan wasan aro.

Dan wasan na cikin tawagar Kamaru da suka je gasar cin kofin duniya a 2010 da 2014 da kuma gasar cin kofin Afirka a 2015 kuma shi ya ci kwallon da ta ba Kamaru nasara a wasan ƙarshe a gasar 2017 a karawa da Masar.

Yanzu Aboubakar na karɓar albashin yuro miliyan shida a shekara a kulub dinsa a Saudiyya.