Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2021: Ba za a yi wasan quater final ba a filin Olembe bayan mutuwar mutane
An sauya wa 'ƴan wasan Kamaru filin da suke wasa daga na Olembe zuwa filin Ahmadou Ahidjo da ke babban birnin ƙasar Yaounde.
An ɗauki matakin ne bayan hasarar rayuka da aka yi yayin da wasu ke ƙoƙarin shiga filin a lokacin da Kamaru ke fafatawa da Comoros ranar Litinin.
Aƙalla mutum takwas ne suka mutu yayin da 38 suka jikkata.
Za a ware minti ɗaya a dukkanin wasannin gasar ta Kofin Ƙasashen Afirka a Kamaru don nuna jimamin waɗanda suka mutu.
Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa da kuma hukumar ƙwallon Afirka Caf sun aike da saƙon jaje ga iyalan waɗanda suka mutu.
Akwai yara biyu cikin waɗanda suka mutun; ɗan shekara takwas da kuma 14, sannan mutum bakwai sun ji mummunan rauni.
Shugaban Caf Patrice Motsepe ya ziyarci waɗanda ke jinya a asibitin Olembe ranar Talata.
Shugaban ya ce alhakin Caf ne da kuma masu shirya gasar kan abin da ya faru tare da ɗaukar matakai domin kauce wa sake aukuwar lamarin.
Filin Olembe da ke ɗaukar 'ƴan kallo 60,000, an taƙaita yawan waɗanda za su shiga kallon wasanni a filin saboda annobar korona.
Amma an ambato hukumomin da ke shirya wasannin na cewa kusan mutum 50,000 sne uka yi ƙoƙarin shiga kallon wasan na Kamaru da Comoros.