Christine Mboma ce aka naɗa Gwarzuwar Ƴar wasa ta BBC ta shekarar 2021

Bayanan bidiyo, BIDIYO: Mboma ce Gwarzuwar Ƴar wasa ta BBC ta shekarar 2021
An wallafa

Ƴar wasan gudu kuma ƴar Namibia Christine Mboma ce aka zaɓa a matsayin wadda ta lashe gasar Gwarzon ɗan wasa na BBC ta shekarar 2021, inda ta zama mace ta farko da ta lashe gasar tun da BBC ta kafa ta.

Ƴar wasan mai shekara 18 da haihuwa ta zama mace ta farko a tarihin ƙasar Namibia da ta lashe lambar azurfa a wasannin Olympics da aka yi a birnin Tokyo na ƙasar Japan a bara.

Ta shaida wa BBC Sport Africa cewa "Ina matukar farin cikin zama ƴar Namibia."

"Ina sadaukar da wannan lambar yabon ga dukkan ƴan Namibia. Wannan kyauta ce ga aiki tuƙurun da na yi."

Mboma ta lashe gasar, inda ta sha gaban ƴan wasan gudu na Kenya Eliud Kipchoge da Faith Kipyegon, da ɗan wasan gudu da tsalle mai naƙasa kuma ɗan Afirka ta Kudu Ntando Mahlangu, da golan kwallon kafa na ƙasar Senegal Edouard Mendy da kuma gwanar ninƙaya ta Afirka ta Kudu Tatjana Schoenmaker.

Ta zama ƴar wasa ta biyu daga ƙasar Namibia da aka yi wa irin wannan karramawar, inda Frankie Fredricks ya lashe gasar ta 1993 wadda BBC ke shiryawa daga shekara zuwa shekara.

Baya ga lambar azurfar da ta lashe na Olympic, Mboma ta kuma sami lambar yabo ta Diamond League bayan da ta lashe gasar ƴan ƙasa da shekara 20 a tseren mita 200 inda ta kara tarihi a gasar da aka yi a bara.