Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Philippe Coutinho: Aston Villa tana cikin masu son zawarcin dan kwallon Barcelona
Aston Villa tana daga cikin kungiyoyin Premier League da ke son zaracin Philippe Coutinho, bayan da dan wasan ke son barin Nou Camp.
Barca na fatan sayar da dan kwallon Brazil, mai shekara 29, bayan da ta dauki Ferran Torres daga Manchester City kan fam miliyan 55.
Kocin Aston Villa, Steven Gerrard na son salon taka ledar Coutinho, wanda suka buga kwallo tare a Liverpool.
Ana kuma alakanta Coutinho da sauran kungiyoyin da ke son daukar dan kwallon ciki har da Arsenal da Everton da Newcastle United da kuma Tottenham.
Coutinho na fatan komawa kan ganiya tun bayan da ya kasa taka rawa a Barcelona wadda ta dauke shi daga Liverpool kan fam miliyan 142.
Koda ya ke dan kwallon ya lashe Champions League a 2020 a Bayern Munich, wadda ta karba aro daga Barcelona, daga baya ya koma Camp Nou.
Idan Barcelona ta rabu da Coutinho za ta samu rara kudi da yawa, bayan da take niyansa albashi mai tsoka, kuma hakan zai sa ta yi wa Torres rigistar buga mata wasanni, wanda ta dauka ranar 28 ga watan Disamba.
Coutinho ya taka rawar gani a Liverpool tare da Gerrard da suka yi tamaula da kadan ya rage kungiyar Anfield ta lashe Premier League a 2014
Gerrard na neman hanyar da zai kara karfin Aston Villa tun bayan da ya maye gurbin Dean Smith daga Rangers a watan Nuwamba, sai dai ya ce ba zai yi gaggawar cefane ba.