Ralf Rangnick: Korona ta hana ni samun ci gaba a Man Utd

An wallafa

Kocin riƙon ƙwarya na Manchester United Ralf Rangnick ya ce tsaikun da korona ta kawo ya yi tasiri ga rashin nasararsa tun karɓar aikin horar da ƙungiyar.

Bajamushen mai shekara 63, ba a doke shi a wasanni huɗu da ya jagoranta tun maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a watan Nuwamba.

Amma ya ce ɓarkewar korona wanda ya kai ga rufe sansanonin atisaye da ɗage wasanni biyu sun dagula masa lissafi.

An tambayi Rangnick ko ya cimma abin da yake buƙata, sai ya ce "aa"

"Duk wani koci ko mai buri - kuma ba ni da banbamci da saura a wannan fannin - yana son samun ci gaba cikin hanzari."

"Amma idan kana son cimma haka, dole sai da atisaye."

Bayan doke Crystal Palace da Norwich da kuma yin kunnen doki da Young Boys a gasar zakarun turai a wasanni Rangnick na farko, an ɗage wasansa da Brentford da kuma Brighton saboda annobar korona.

Wasansa da Newcastle a ranar Litinin, Rangnick ya ce "ban ji daɗin rawar da ƴan wasa suka yi ba" yayin da ya fita da maki ɗaya a St James' Park bayan tashi wasan 1-1.