Premier League: An kara soke wasa hudu a babbar gasar Ingila

An wallafa

Mahukuntan gasar Premieer League sun sanar da dakatar da wasa hudu daga wanda za a buga a karshen mako, don gudun yada cutar korona.

Wasannin da aka soke sun hada da na Southampton da Brentford, Watford da Crystal Palace, West Ham da Norwich da na Everton da Leicester City.

A ranar Alhamis an dakatar da wasan da ya kamata Leicester City ta karbi bakuncin Tottenham a King Power da wanda ya kamata a fafata tsakanin Manchester United da Brighton ranar Asabar.

Kenan tun daga tsakiyar mako an dakatar da wasu wasannin Premier League har da na Leicester City da Tottenham.

'Yan wasan Liverpool da suka hada da Fabinho da Curtis Jones da Virgil van Dijk ba za su buga karawa da Newcastle ba ranar Alhamis, bayan da ake zargin sun kamu da cutar.

To sai dai kuma mahukuntan gasar sun yi watsi da batun a dakatar da wasannin karshen mako, inda ta fitar da sanarwa cewa ''Dukkan wasannin da aka tsara yi a karshen mako za a buga ssu kamar yadda aka tsara.''

Kimanin wasa tara aka dakatar tun daga makon da ya wuce ciki har da na Tottenham da Brighton ranar Lahadi da na Brentford da Manchester United ranar Talata da kuma na Burnley da Watford ranar Laraba.

Chelsea ma na fuskantar kalubalen cutar korona da ta kama wasu 'yan wasanta, amma ba a soke wasanta da Everton ba karawar mako na 17.