Sergi Roberto: Barcelona za ta yi wa dan wasanta tiyata

An wallafa

Barcelona ta sanar da cewar likitoci za su yi wa Sergi Roberto tiyata a raunin da yake damunsa a kafarsa ta hagu.

Dakta Lasse Lempainen zai yi aikin a Turku a Finland tare da kulawar likitocin Barcelona, haka kuma kungiyar ta ce za ta sanar da sauran bayanai kan lokacin da zai yi jinya, idan an yi masa aikin cikin nasara.

Duk da raunin da yake damun Roberto ya buga wa Barcelona wasa 12 a kakar nan, inda tara daga ciki a La Liga da kuma fafatawa uku a Champions League.

Shine ya ci wa Barcelona kwallon farko da fara La Liga a karawar da ta yi nasara da ci 4-2 a kan Real Sociedad a Camp Nou da kuma 2-1 da ta doke Getafe.

Barcelona tana mataki na bakwai a kan teburin La Liga da maki 23 da kwantan wasa daya a teburin da Real Madrid ke jan ragama da maki 36.

Ranar Asabar Barcelona za ta karbi bakuncin Real Betis a karawar mako na 16 a babbar gasar Sifaniya a kuma ranar Real Madrid za ta ziyarci Real Sociedad a wasan hamayya.