An dakatar da alkalin da ya hura wasan Argentina da Brazil

An wallafa

Hukumar kwallon kafa ta Kudancin Amurka CONMEBOL ta dakatar da alkalin wasan da ya hura karawa tsakanin Argentina da Brazil a karawar neman gurbin higa gasar cin kofin duniya

Haka kuma ta sanar da dakatar da wanda ya kula da na'uar da ke taimakawa alkalin wasa yanke hukuncin wato VAR a karawar ta ranar Talata a Argentina.

Ana tsaka da wasa mai tsaron bayan Argentina, Nicolas Otamendi ya yi wa Raphinha gula a baki - hakan ya sa aka bar dan wasan Brazil kwance baki da jini a cikin fili - amma kuma alkalin wasa bai yi hukunci ba, wanda ke kula da VAR bai bukaci a sake duba laifin ba.

Ran kocin Brazil, Tite ya baci, wanda ya ce abu ne mai wahala mai kula da VAR bai ga abinda ya faru ba, kan gula da Otemendi ya yi wa Raphinha.

CONMEBOL ta sanar cewar ta duba yadda alkalin wasa Andres Ismael Cunha Soca Vargas da mai kula da VAR, Esteban Daniel Ostojich Vega suka gudanar da aikinsu da cewar sun tafka kura-kurai. Hukumar ta sanar da dakatar da alkalan biyu nan take.

Sakamakon wasan da suka tashi ba ci a ranar Talata ya sa Brazil da Argentina sun samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su wakilci Kudancin Amurka a Qatar a 2022, duk da ba a kammala wasannin ba.