Paul Pogba: Dan wasan Man Utd ya ji raunin a wajen atisayen France

Paul Pogba is sent off in Manchester United's match with Liverpool at Old Trafford

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Paul Pogba bai yi wa Manchester United wasa ba, tun bayan jan kati ranar 24 ga watan Oktoba a karawa da Liverpool
An wallafa

Dan wasan Manchester United, Paul Pogba, ba zai buga wa Faransa wasanni biyu da suka rage mata a neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ba.

Dan kwallon mai shekara 28 ya ji rauni a lokacin atisaye ranar Litinin, kamar yadda hukumar kwallon kafar Faransa ta sanar.

Saboda hada ba zai buga wasan da Faransa za ta karbi bakuncin Kazakhstan ranar Asabar da wanda za ta ziyarci Finland ranar 16 ga watan Nuwamba ba.

Haka kuma ba zai yi wa United karawar Premier League da Watford ba ranar 20 ga watan Nuwamba, wasa na uku da zai kammala hukuncin dakatar da shi da aka yi.

Pogba ya karbi jan kati a wasan da Liverpool ta doke United a Old Trafford da ci 5-0 ranar 24 ga watan Oktoba.

Tawagar Faransa na bukatar maki daya daga karawa biyu da ta rage mata domin kai wa gasar cin kofin duniya da Qatar za ta karbi bakunci a 2022.

United karkashin Ole Gunnar Solskjaer na fama da 'yan wasa da ke jinya da suka hada da Raphael Varane da Edinson Cavani da kuma Luke Shaw.