Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Old Wulfrunians ta ci Lane Head 19-18 a bugun fenariti
Wasu kungiyoyin da ke buga gasa a Midlands sun kafa tarihin cin kwallo 44 a bugun daga kai sai mai tsaron raga a Ingila.
Tarihin da ake da shi a baya shine na cin kwallo 34 da aka yi a wasa tsakanin matasan Chelsea 'yan kasa da shekara 23 da Oxford United a gasar EFL Trophy.
Na biyun kuwa shine tsakanin Taunton Town da kuma Truro City a gasar Kudanci ta Challenge Cup da aka ci fenariti 34 a karawar.
Sai wannan karawar ta Old Wulfrunians daga Wolverhampton da Lane Head daga Bloxwich da suka kafa sabon tarihi.
Tun farko sun tashi 3-3 a gasar JW Hunt Cup zagayen farko daga nan ta kai ga bugun daga kai sai mai tsaron raga da Old Wulfs ta yi nasara da ci 19-18 wato kwallo 44 kenan suka buga jumulla.
An fara buga gaasar JW Hunt Cup tun daga 1926.