Fifa ta dage wa Chadi haramcin yin wasa da wasu kasashen

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon ƙafa ta duniya Fifa ta ɗage haramcin da ta sa wa ƙasar Chadi na yin wasa da wasu ƙasashen, wanda aka sanya mata saboda katsalandan ɗin da gwamnatin ƙasar ke yi cikin harkokin wasanni.
Chadi ta shafe wata shida ƙarƙashin wannan haramci.
Fifa ta sanya wannan haramci ne a kan Chadi bayan da ministan matasa da wasanni ya soke hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasar a watan Maris.
"Hukumar Fifa ta yanke shawarar ɗage haramcin ba tare da ɓata lokaci ba," a cewar Fifa a wata sanarwa ta ranar Talata.
An bayar da wasu dalilai kan kawo ƙarshen haramcin kamar haka:
- Hukumomin Chadi sun mayar da shugabannin hukumar wallon ƙafar kasar ta FTFA
- Hukumomin Chadi sun soke matakinsu na kafa kwamitin wucin gadi na shugabancin harkokin ƙwallon ƙafa
- Harabar hukumar FTFA ta sake koma wa ƙarƙashin ikon Shugaba Moctar Mahamoud.
"Sakamakon ɗage haramcin, za a tura wata tawaga ta jami'an Fifa da Caf zuwa N'Djamena ba tare da ɓata lokaci ba wajen tattauanwa da FTFA da gwamnatin Chadi," Fifa ta ƙara da cewa.
Bayan da gwamnati ta soke FTFA ne sai hukumar kwallon kafa ta Afirka ta dakatar da Chadi daga buga wasanni biyu na neman shiga Gasar Kofin Afirka.







