Manuel Neuer bai yi atisaye a tawagar Jamus ran Talata ba

An wallafa

Kyaftin din tawagar kwallon kafar Jamus, Manuel Neuer bai yi atisaye ranar Talata tare da 'yan wasa ba.

Jamus na shirye-shiryen buga wasannin shiga gasar cin kofin duniya da Romania da kuma Arewacin Macedonia cikin watan Oktoba.

Kyaftin din na jinyar raunin da ya ji tun bayan kammala wasan da Eintracht Frankfurt ta yi nasara 2-1 a gidan Bayern Munich ranar Lahadi a gasar Bundesliga.

Koci, Hansi Flick ya yi atisaye da 'yan wasa 22 a filin wasa na SV Hamburg mai buga karamar gasar Jamus ta biyu.

Da kyar ne idan Neuer zai samu buga wasan da Jamus za ta karbi bakuncin Romania ranar Juma'a, sannan kwana uku tsakani ta je Skopje.

Tawagar Jamus tana ta daya a kan teburin rukuni na tara, za kuma ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a Qatar a 2022, amma ya danganta da sakamakon wasannin nan.