Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Suarez ya ci Barcelona ya kara jefa ta cikin matsi
Atletico Madrid ta hada maki iri daya da na Real Madrid a mataki na daya a kan teburin La Liga, bayan da ta doke Barcelona 2-0.
Barcelona ta yi rashin nasara ne a gidan Atletico a karawar mako na takwas da suka fafata ranar Asabar, wanda hakan ya kara jefa kungiyar Nou Camp cikin matsi, wadda ke fuskantar kalubale a bana.
Thomas Lemar ne ya fara cin kwallo daga baya tsohon dan wasan Barcelona, Luis Suarez ya zura na biyu a raga.
Shima Antoine Griezmann dan kwallon Barcelona da ke buga wasannin aro a tsohuwar kungiyarsa Atletico ya shiga karawar daga baya.
Duk da matsalar da Barcelona ta fada, wannan shine karon farko da ta yi nasara a karon farko a La Liga - sai dai hakan ya sa ta koma ta takwas a kan teburi da maki 12 da tazarar maki biyar tsakaninta da Atletico, wadda take ta biyu da rarar kwallaye tsakaninta da Real Madrid, amma da maki iri daya.
Kafin wasan da Atletico ta doke Barcelona, kungiyar Nou Camp ta ci wasa uku da canjaras uku, an kuma doke ta wasa biyu a jere a Champions League, kuma duk da kwallaye uku-uku aka zura mata a raga.
Atletico Madrid za ta buga wasan gaba ranar 17 ga watan Oktoba, inda za ta ziyarci Granada, ita kuwa Barcelona za ta karbi bakuncin Valencia a dai ranar da Atletico za ta fafata.