Abin da ya kamata ku sani kan wasan Liverpool da Man City

Klopp Guardiola

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan mako na bakwai a gasar Premier League da za su fafata ranar Lahadi a Anfield.

Kungiyar Anfield za ta buga wasan na hamayya ba tare da Trent Alexander-Arnold ba, wanda bai yi mata wasan da ta casa FC Porto a Champions League ranar Talata.

Haka kuma har yanzu Thiago da kuma Harvey Elliott na jinya, ba za su buga wa Liverpool daya daga babban wasa a gasar Ingila ba.

Shi kuwea Guardiola zai ja ragamar fafatawar ba tare da Ilkay Gundogan da kuma Oleksandr Zinchenko, wadanda ke jinya.

Liverpool tana da maki 14, ita kuwa Manchester City maki 13 ne da ita, bayan da kowacce ta yi karawa shiga a Premier League ta bana.

Wasa tsakanin kungiyoyin biyu:

Kungiyoyin biyu sun kara a bara, inda suka tashi 1-1 a Etihad a gasar Premier League ranar 8 ga watan Nuwambar 2020 a fafatawa ta biyu a gasar City ta je Anfield ta ci 4-1 ranar 7 ga watan Afirilun 2021.

Nasarar da City ta yi a bara a Anfirld ta kawo karshen wasa 17 a waje da Liverpool ba tare da yin nasara ba, bayan canjaras biyar aka doke ta 12.

City za ta iya samun nasara a kan Liverpool a Anfiled sau biyu a jere a karon farko, tun bayan doke ta sau hudu da ta yi tsakanin 1935 to 1937.

Liverpool ta yi nasara ne a wasa daya daga bakwai baya da suka fafata da City a dukkan karawawa, wadda ta yi canjaras uku da rashin nasara uku.

Kokarin Liverpool:

Liverpool ce kadai wadda ba a ci ba a gasar Premier League ta bana, wadda ta ci wasa hudu da canjaras biyu.

Wasa 16 da ta yi idan ka hada tun daga bara ba a doke ta ba, shine mafi tsawo da wata kungiya ta yi bajinta a manyan gasar Ingila hudu, wadda ta yi canjaras hudu da cin wasa 12.

Mohamed Salah ya ci kwallo hudu a karawa biyar da Manchester City a Anfield a dukkan fafatawa.

Ba a doke Liverpool ba a wasa 50 da Virgil van Dijk ya yi a Anfield, inda aka ci wasa 44 da canjaras shida da shi a cikin karawa.

Kwajon Manchester City:

Watakila Manchester City ta kafa tarihin yin wasa shida a jere ba tare da kwallo ya shiga ragarta ba.

Wasa uku da ta buga a waje, sakamakon kan tashi 1-0 ne a bana, bayan rashin nasara a Tottenham da wanda ta je ta doke Leicester and Chelsea.

Kwallo 12 da City ta zura a raga 'yan wasanta tara ne suka ci mata su, Chelsea ce kan gaba mai 'yan wasa 10.

Watakila Fernandinho ya zama na biyu dan kasar Brazil da ya buga wasa 250 a Premier League, bayan Willian.

Pep Guardiola ya sha kashi sau takwas a fafatawar da ya fuskanci Jurgen Klopp a kowacce gasa.