Barcelona za ta ziyarci Atletico Madrid a matsanancin hali

Asalin hoton, Getty Images
Atletico Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na takwas a gasar La Liga da za su kara ranar Asabar.
Sai dai kungiyar ta Nou Camp za ta je wasan bayan kalubalen da take fuskanta a wasannin bana.
Za kuma ta buga karawar ba tare da kocinta, Ronald Koeman ba, wanda aka dakatar wasa biyu, bayan jan kati da aka yi masa a fafatawa da Cadiz.
Koeman bai halarci wasan da Barcelona ta doke Levante 3-0 ba a gasar La Liga ranar Lahadi 26 ga watan Satumba a Nou Camp.
Barcelona ta ci wasa daya daga biyar da kara a dukkan fafatawa, an kuma doke ta 3-0 a Benfica ranar Laraba a Champions League.
Tuni ake hasashen cewar da zarar Barcelona ta yi rashin nasara a Atletico ranar Asabar, zai zama karshen Koeman kenan a kungiyar.
Barcelona wadda keda kwantan wasa daya, Real Massdrid ta bata tazarar maki biyar mai jan ragamar wasannin bana.
Kyaftin din Barcelona, Sergio Busquets ya ce 'yan wasa sun taka rawar da kungiyar ta shiga wannan mawuyacin halin da suke ciki.
''Koda an kori koci ba zai kawo karshen halin da muka tsinci kanmu ba, '' in ji Busquets ''Amma duk muna da laifi. Idan za a fadi gaskiya, muna fuskantar kalubale.''
Koeman ya ce yana da tabbacin 'yan wasa suna tare da shi, suna iya kokarinsu, amma bai da tabbaci idan mahukunta za su ci gaba da bashi dama ba.
''Zan iya sanar da ku ra'ayi na kan aikin da nake gudanarwa da cewar 'yan wasa suna goyon bayana, suna iya kokarinsu, '' in ji kocin dan kasar Netherlands.
''Ban san matsayin shugabannin Barcelona ba a kaina, ba zan yi magana da yawa kan makoma ta ba a kungiyar, domin ban san tunaninsu a kaina ba.''
Barcelona za ta je karawar ba tare da Jordi Alba ba, kuma idan kungiyar Nou Camp ta yi nasara za ta hau kan Atletico wadda take ta hudu a teburi, sauran wadanda ba za su yi wa Barcelona karawar ba sun hada da Sergio Aguero da Martin Braithwaite da kuma Ousmane Dembele.
Barcelona ta yi rashin nasara a wasa biyu a Champions League, bayan da Bayern Munich ta fara doke ta 3-0 a Sifaniya.
Kenan ba ta da maki ko daya kenan bayan wasa biyu, an kuma zura mata kwallaye shida ba tare da cin koda daya ba.










