Cristiano Ronaldo zai buga wa Portugal wasa uku a Satumba

Cristiano Ronaldo

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Koci Fernando Santos ya ce Cristiano Ronaldo zai buga wa Portugal wasa uku da za ta kara cikin watan Satumba.

Ranar Talata kyaftin din tawagar Portugal ya kammala komawa Manchester United daga Juventus, bayan da ya taka leda a Old Traford tsakanin 2003 zuwa 2009.

Portugal za ta fafata da Jamhuriyar Ireland a wasan neman shiga gasar kofin duniya ranar Laraba, sannan ta buga wasan sada zumunta da Qatar ranar Asabar, sai ta karkare da karawar neman shiga gasar kofin duniya da Azerbaijan ranar Talata.

Ronaldo na daf da kafa tarhin yawan ci wa tawaga kwallaye, bayan da Ali Daei ke rike da tarihin mai 109 a raga.

Kyaftin din Portugal ya zura kwallo 674 a fafatawa 895 a gasar Turai daban-daban.

Cikin kwallaye 674 da ya zura a raga ya ci da kafar hagu da 110 da kai da kuma 440 da kafar dama.

Ronaldo wanda ya lashe Ballon d'Or karo biyar da zama kan gaba a cin kwallaye a Champions League da ya zura 134 a raga a wasa 176, inda Lionel Messi ke biye da shi a mataki na biyu.