Barcelona ta bai wa Ansu Fati rigar Messi mai lamba 10

An wallafa

Kungiyar Barcelona ta sanar da bai wa Ansu Fati riga mai lamba 10, wadda Lionel Messi ya yi amfani da ita a kungiyar.

Barcelona ta tambayi dan kwallon mai shekara 18 ko zai iya daukar nauyin da rigar take da shi a kungiyar, wanda ya amsa ya shirya.

Tun farko an dauka cewar Philippe Coutinho ne zai karbi rigar, idan aka tabbatar zai ci gaba da taka leda a kungiyar, sai dai dan kwallon Brazil din bai sha'awar hakan.

Ba a dai samu wanda ya yi kwadayin saka riga mai lamba 10 a Barcelona ba, dalilin da ya sa kungiyar ta tuntubi Ansu Fati, wanda ya amince nan take.

Ansu Fati wanda rabon sa da taka leda tun cikin watan Nuwambar 2020 na fatan komawa taka leda, bayan jinyar rauni a gwiwa da likitoci suka yi masa aiki karo hudu.

Cikin watan Agusta Lionel Messi ya bar Barcelona wadda ya yi kaka 21 a kungiyar, ya koma Paris St Germain kan yarjejeniyar kaka biyu.

Kyaftin din Argentina, wanda ya lashe Ballon d'OR karo shida ya karbi lamba 10 a Barcelona tun bayan da Ronaldinho ya bar Camp Nou a 2008.

Fati shine matashin da ya ci kwallo a Barcelona a Agustan 2019 a wasa da Osasuna, yana da shekara 16 da kwana 304 a lokacin.

Tun daga nan ya kara zura 12 a raga a wasa 42 a dukkan fafatawa da ya buga mata, tun bayan da ya koma Camp Nou yana da shekara 10.

Cikin wadanda suka sa riga mai lamba 10 a Barcelona suka yi fice a fannin tamaula a duniya sun hada da Rivaldo da kuma Romario.

Cikin sauye sauyen lambar riga da Barcelona ta yi wa 'yan wasanta a bana, Ousmane Dembele ya karbi lamba 11.

Yusuf Demir ya karbi wadda Dembele ya saka a baya, shi kuwa sabon dan kwallon da ta dauka Luuk de Jong ya karbi riga mai lamba 17.