Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Edinson Cavani: Man Utd ta dauki tsohon dan kwallon PSG
Manchester United ta kammala daukar tsohon dan kwallon Paris St-Germain, Edinson Cavani a matakin mai cin gashin kai.
Mai shekara 33 dan kwallon tawagar Uruguay wanda ya bar PSG a watan Yuni, ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka daya.
Cavani ya ci kwallo 341 a wasa 556 da ya yi kungiyoyi har da 200 da ya zura a raga a karawa 301 da ya yi wa PSG. Ya kuma ci wa kasarsa kwallo 50 a fafatawa 116 da ya yi mata.
Daya daga wasan da ake sa ran Cavani zai buga wa United shi ne haduwa da PSG a Champions League karawar cikin rukuni ranar 20 ga watan Oktoba.
Kafin nan kungiyar ta Old Trafford za ta je Newcastle United a gasar Premier League ranar 17 ga watan Oktoba.
Kungiyar da Ole Gunnar Solskjaer ke jan ragama tana ta 16 a kasan teburin Premier, bayan da Tottenham ta doke ta 6-1 ranar Lahadi a Old Trafford.